<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><author>Daniel Towner, John H. Sammis</author>
<lyrics>[V1]
 1) Muna tafiya yau cikin hanyar Yesu.
 Amma ba mu kaɗai ba ne fa.
 Yesu ma yana nan, yana tare da mu,
 Gama shi yana ja gabanmu.

[V2]
 KORUS
 Kai dai ka zo, ka je tare da mu,
 Cikin hanyar Mai Ceto, zuwa wurin Allah

[V3]
 2) Cikin ƙuncinmu duk, ya kan tallafe mu,
 Yana ƙarfafa zukatanmu.
 Ko jaraba ta zo, zai yi hanyar tsira,
 Masu Bi duk su ci nasara.
 Korus

[V4]
 3) Da abinci mai rai cikin Maganarsa
 Ya kan ciyad da kowannenmu,
 Kamar maƃulƃulai na ruwa mai rai
 Ruhunsa yana cikinmu duk.
 Korus

[V5]
 4) Ya yi alkawari, za ya ji roƙonmu,
 In mun yi cikin sunan Yesu.
 Sai mu ƙaunace shi, mu bi dokokinsa,
 Sai mu bi shi da zuci ya ɗaya.
 Korus</lyrics>
<title>Muna Tafiya Yau Cikin Hanyar Yesu LW212</title>
<hymn_number>212</hymn_number>
</song>